Wednesday, January 22, 2020

Bayani Akan Zazzabin Lassa (Lassa Fever)

Aliyu Abubakar  |


A cikin makon nan ne aka samu 'bullar zazzabin Lassa a jihar kano da yayi sanadiyar mutuwar wasu mutane tare da wasu ma'aikatan lafiya, kasantuwar haka yasa muka kawo muku wannan bayanin domin wayar da kan al'umma akan cutar da kuma hanyoyin da za'abi domin kare kai.

Zazzabin Lassa na daya daga cikin jinsin jinyoyin da ake kira da 'Rodent-borne Hemorrhagic fever' a turance ma'ana jinyoyin da ake dauka daga kananan dabobi irinsu beran gida wato 'Mastomys natalensis' wanda shine kusan ginshiki wajen yada cutar ga mutane sakamakon wata kwayar virus dake da hatsarin gaske da yake dauke ita, mafi yawanci wannan jinya tafi yaduwa a 'kasashen dake yammacin Afrika da kusan kaso 36-67 cikin100.
An fara samun bullar wannan cuta a Nigeria a 'kauyen Lassa dake jihar Borno a shekarar 1969 a wanni sansanin Amurikawa, alkaluman kididdiga na hukumar lafiya ta duniya (WHO) ya nuna cewa kimanin mutane 300,000 dake yammacin Afrika ke kamuwa da zazzabin Lassa a duk shekara kuma a 'kalla mutane 5000 ne ke mutuwa a kowace shekara.

Yadda zazzabin Lassa ke yaduwa

Zazzabin Lassa na yaduwane ta daya daga cikin wadannan hanyoyin:
• Cin abinci ko abin shan da bera yayi kashi ko fitsari aciki
• Sha'kar iskar da take gurnace da kashi ko fitsarin bera
• Cin naman beran dake dauke da wannan 'kwayar cutar
• Taba yawu, jini ko majina na mutumin da jinyar ta baiyana a jikinsa, amma indan alamun basu baiyana ba to taba wadannan abubuwan baza susa mutum ya kamu da jinyarba, haka kuma mu'amalar jiki da jiki da mai jinyar irinsu gaisuwa ko runguma basa sa a kamu da jinyar.

Alamomin zazzabin Lassa

'Kwayar cutar zazzabin Lassa na iya ratsa ko ina a jikin dan-Adam, Alamun na fara baiyana ne bayan sati 1-3 da kamuwa da 'kwayar cutar, alamomin cutar sun kasance kamar haka:

√ Mataki na farko wanda shine ke dauke da kusan kaso 80 cikin 100 na alamun jinyar ya hada da tsananin zafin jiki, tsanin gajiya da kuma tsananin ciwon kai.
√ Mataki na biyu shine ya dauki kusan kaso 20 cikin 100 na alamun jinyar Wanda ya hada da ciwon jiki, kurajen jiki da na baki, lalacewar koda ko zuciya, amai, ciwon baya da na kirji, shan numfashi da kyar, ciwon ciki da kuma gudawa mai jini aciki a wasu lokutan mutum na iya rasa jinsa.
√ Mataki na uku shike dauke da kaso 15 cikin 100 na alamun jinyar wanda ya hada da kumburin fuska sai kuma zubar jini ta baki, hanci da kuma farji ga mata, mafi ya wanci ba'a cika rayuwa ba idan akazo wannan matakin, da zarar mutum ya fara jin days daga cikin alamomin da muka ambata a matakin farko da ya garzaya zuwa asibiti domin daukar matakin gaggawa.

Hanyoyin kariya daga zazzabin Lassa

Matakan kariya daga zazzabin Lassa sune kamar haka:

√ Mataki na farko ya hada da matakan kariya da ake bi Kafin akamu da jinyar wanda suka hada da:
• Kula da tsaftar muhalli
• Kora ko toshe duk wata hanyar shigar bera gidajenmu
• A daina barin abinci ko kwanuka a bude idan dare yayi
• Rufe hanci da kyalle yayin da ake share kashin bera ko fitsarinsa
• Zuwa asibiti da zarar zazzabi ya wuce kwana biyu

√ Mataki na biyu ya hada da matakan da ake bi bayan kamuwa da jinyar wanda suka hada da shan maganin dake kashe kwayar cutar virus wato (antiviral drugs) irinsu Ribavirin dasauransu.

Allah ya 'Kara karemu.
©GHN

No comments:

Post a Comment