Sunday, January 19, 2020

Bayani Akan Ciwon Olsa (Peptic Ulcers)




Nuraddeen Abba Mustapha  |

Ciwon Olsa (Peptic Ulcers) daya ce daga cikin ciwuka da dake addabar sashen da ya shafi ciki da ake kira da (gastrointestinal tract) a turance, mafi ya wanci akan kira olsa da gyambon ciki sakamakon tafi kama tumbi, karamin hanji da kuma kwararon ma'kogoro wato (Oesophagus).

Yadda Ciwon Olsa ke faruwa

Ciwon olsa na faruwa ne yayinda bangon kariya wato (gastrointestinal barrier) da ya katange sassan hanji ko tumbi ya samu rauni ko ya kuje, amfanin wannan bangon kariyar shine bada kariya ga kafofin jini na jiki daga dukkanin wani abu da yake a cikin tumbi ko hanji.

Abubuwan da suke kawo Ciwon Olsa

√ 'Konewar sinadarin Hydrochloric acid wanda ake samarwa a tumbi don narkar da abinci, 'konewar wannan sinadarin shi kesa bangon kariya na tumbi ko hanji ya sami rauni
√ Kamuwa da 'kwayar cutar Bakteriya da ake kira da Helicobacter pylori (H pylori)
√ Yawan amfani da nau'ikan magungunan rage jin zafi ko zugi da ake kira Non-steroidal anti-inflammatory drugs (NSAID) irinsu Diclofenac, Ibuprofen dasauransu, cikakken bayani zaizo a rubutun mu na gaba kan illolin amfani da wadannan magungunan
√ Yawan ci ko shan abubuwan da suke 'kunshe da sinadarin caffeine acikinsu da ya wuce kimanin >400mg a rana
√ Shan Barasa
√ Damuwa mai tsanani
√ Rashin cin abinci akan lokaci musamman Karin safe
√ Cin abincin da yake da mai'ko ko abin sha mai tsami sosai

Abubuwan da muka ambata asama na farko da na biyu Kai tsaye suna samar da rauni/ciwo ga bangon kariya ta hanyar rarake kariyar (barrier), Sauran abubuwan kuma suna haifar da Ciwon Olsa ne ta wata hanyar daban wadda ta shafi sinadarai na jiki.

Alamomin ciwon olsa

√ Yawan jin Amai
√ Rashin sha'awar abinci
√ 'Kuna a 'kirji ko zafin ciki
√ Fitar da jini daga tumbi ko hanji
√ Yawan gyatsa, magwas, da kuma danka ko kumburin ciki
√ Ramewa ta rashin dalili
√ Ciwo ta 'bangaren baya musamman yayin cin abinci

Hanyoyin Kariya daga Ciwon Olsa

√ Rage yawan amfani da kayayyakin 'kanshi ko yaji a abinci domin suna dauke da sinadarin dake faama ciwo da ake kira da Capsiasin
√ Daina shan Taba Sigari da kuma Barasa, tare da Nisantar abubuwan dasuke 'kunshe da sinadarin caffeine a ciki
√ Cin abincin da ya hada da ganyayyaki da kuma kayan marmari.
Kiyaye wadannan matakan da muka ambata na kariya na taimakawa wajen rage kamuwa da Ciwon Olsa.

Magungunan Ciwon Olsa

Ciwon olsa akan iya maganceshi ta hanyoyi da dama mafi sauki shine ta hanyar shan magunguna, Magunguna olsa ana amfani da sune kawai bayan rubutawar likita idan aka yi gwajin ciwon olsa akan mara lafiya kuma aka tabbatar da cutar ta hanyoyi da dama da suka hada da gwajin da da ake haska cikin mutum wato Endoscopy/Gastroscopy da kuma gwajin kwayar Bacteriya ta H pylori da ake amfani da Jini ko Bahaya na mutum da dai sauransu.
Magungunan magance Ciwon Olsa sun hada da:

√ Nau'in maganin da ake kira da Antibiotics: Idan akayiwa mutum gwajin jini ko bahaya na kwayar bacteriyar H pylori sakamakon gwajin ya nuna cewa akwai samuwar wannan 'kwayar bacteriyar dake sa ciwon olsa, za ayi amfani da a 'kalla kala biyu na wannan jinsin maganin da suka hada da; Tetracycline, Metronidazo, Amoxicillin, clarithromycin, za ayi amfani dasu sau biyu a rana na tsahon sati biyu domin kashe 'Kwayar cutar.
           
√ Magungunan rage yawan sinadarin narkar da abinci da jiki yake samarwa wato (Hydrochloric acid) wanda  suka hada da:
• Nau'in maganin da ake kira da Proton pump blockers (PPIs) irinsu Omeprazole, Pantoprazole, Lansoprazole
• Nau'in maganin da ake kira da Antihistamine drugs/H2-receptor antagonists irinsu Cimetidine , Ranitidine, Nizatidine
• Nau'in maganin da ake kira da Mucous lining protectors irinsu Sucralfate ( carafate)
• Nau'in maganin da ake kira da Mucus and HC03 producing drugs irinsu misoprostol
• Nau'in maganin da ake kira da Antacids irinsu Gestid, Gelusil da kuma nau'in maganin da ake kira Alginates da sauransu. A takaice mai ciwon olsa akan dorashi akan tsarin da ake kira da Triple Therapy ma'ana zaiyi amfani da magani kala uku alokaci daya biyu daga ciki zasu yaki 'kwayar bakteriyar H pylori dayan kuma zai hana fitowar sinadarin Hydrochloric acid daga jiki, shan wadannan magungunan daidai da yadda likita ya tsara zai taimaka wajen rabuwa da jinyar.

Shan maganin rage jin radadi ko zugi wato (NSAID) kamar yadda muka ambata a baya na daga cikin nau'ikan magungunan dake haifar da ciwon olsa saidai idan ya zama ba makawa sai anyi amfani dasu to a iya amfani da wadanda suke da dama-dama cikinsu da ake kira da COX-2 inhibitor irinsu Celebrex, kuma ana iya amfani da Paracetamol domin rage zafin radadin ciwon olsa.

Ginsau HealthNetwork a shirye suke domin amsa tambayoyin ku ko baku shawarwari da suka shafi ingancin lafiyarku, muna rokon Allah daya 'karamana lafiya.

Mungode
©GHN

No comments:

Post a Comment