![]() |
| Aliyu Abubakar | |
<> SHIN ANA GADON CIWON SUGA?
Daga: Aminu gbr
E, ana gadon ciwon suga nau'i na biyu daga cikin ire-iren ciwon suga da mukayi bayani, duk da cewa ana iya gadonsa, halayya ta fi tasiri musamman dabi’ar ciye-ciyen abinci da yanayin jikin mutum, don haka idan iyayenka na da nau’i na biyu na ciwon suga ba a sa ran za ka kamu, sai dai idan dabi’ar ciye-ciyenka ce za ta sa ka kamu.
<> SHIN MAI CIWON SUGA ZAI IYA SHAN RAKE?
Daga: Hafsat Ahmad
E, mai ciwon suga na iya shan rake saboda sinadarin sugan da yake 'kunshe dashi bashi da karfi sosai wajen cutatar da mutum, sinadarin sugan dake cikin rake ana kiransa da fructose, shikuma fructose yana cikin jerin sugan da suke da low glycemic index, don haka nauyin sugan dake cikinsa bai kai ya ace zai cutar ba sai dai zuwa wani lokaci idan aka fiya amfani dashi zai iya zama illa, zaifi kyau mai ciwon suga ya maida hankali kan cin ganyayyaki da kuma 'ya'yan itatuwa kamar yadda mukayi bayani akan tsarin abincin masu ciwon suga.
<> SHAZUMAMA NA BIN FITSARINA SHIN WANNAN NA NUNA CEWA INA DA CIWON SUGA?
Daga: Ali Muh'd
A'a, haka baya nuni da cewa kana da suga saboda shazumama ba wai sai fitsarin mai suga yake biba, amma dai idan aka cika ganin haka, alama ce dake nuns cewa akwai bukatar yin gwaji domain tabbatar da abin da ake tunani.
<> TAFIN KAFATA NA YAWAN YIMIN ZAFI KUMA GA YAWAN YIN FITSARI MAI ZAFI SHIN WANNAN NA NUNA CEWA INA DA CIWON SUGA?
Daga: Yahaya Suleiman
Wadannan alamu tabbas ciwon suga na iya haifar dasu amma annan alamu kaitsaye ba a ce na ciwon suga ba ne, domin sun fi kama da shigar kwayoyin cuta cikin mafitsara, shawara anan shine da ka garzaya asibiti aima aune-aunen fitsari da jini domain banbancewa.
<> NI INA DA YAWAN SHAN RUWA KO HAKAN NA NUFIN INA DA CIWON SUGA?
Daga: Yahaya Suleiman
E, wannan na daya daga cikin alamun ciwon suga da muka ambata idan ka koma rubutun da mukayi akan ciwon suga, dan kasan wannan alama ta yawan yin fitsari ga mai ciwon suga kusan itace gaba fiye da yawan shan ruwa, don haka saika garzaya asibiti domin a yi maka gwaje-gwaje.
<> INANE YA KAMATA NAJE DOMIN GWAJIN SUGA?
Daga: Yakubu Dahiru Gatafa
Toh, Idan kanajin daya daga cikin alamun da muka ambata na ciwon suga sai kayi maza kaje asibiti kaga likita, zai turaka dakin gwaji domin tabbatar da jinyar daga baya ya doraka akan tsarin da take daidai da matakin jinyarka.
Mungode da kulawarku, dafatan zaku cigaba da kasan cewa tare damu, kuma ashirye Muke domin amsa tambayoyin ku akoda yaushe.
©GHN

No comments:
Post a Comment