![]() |
| Nura Idris | |
Dabbobi na taka muhimmiyar rawa a rayuwar mu musamman ta bangaren samar da nishadi da kuma kasancewar wasu daga cikinsu abinci garemu, sai dai a wasu lokutan sukan zama babban jigo na yaduwar jinyoyi ga mutane sakamakon 'kwayoyin cutar bacteria, fungi, parasite da kuma virus da suke dauke dasu, kamuwar dabbobi da daya daga cikin wadannan 'kwayoyin cutar zaisa ta'ammuli dasu ya zama barazana ga lafiyar dan-Adam, sakamakon zasu iya yada wadannan 'kwayoyinn cutar zuwa ga mutane, ire-iren cututtukan dake yaduwa daga dabbobi zuwa mutane sune ake kira da 'zoonoses' ko kuma 'anthropozoonoses diseases' a turance, kuma ko wane bangare na dabobi (na gida da na daji, manya ko 'kanana) na iya yada jinyoyi ga dan-Adam matukar sun kamu da daya daga cikin wadancan 'kwayoyin cutar da muka ambata.
Hasashen hukumar lafiya ta duniya (WHO) ya nuna cewa Kimanin kaso 61 cikin 100 na jinyoyi ana samun sune daga dabbobi haka zalika kimanin kashi 75 na sababbin jinyoyin dake 'bulla a duniya daga dabobi suke, hakan ke nuna cewa mutane sama da miliyan 50 ke kamuwa da ire-iren jinyoyin da ake samu daga dabbobi a duk shekara kuma a 'kalla mutane sama da mutane 230,000 ke mutuwa a ko wace shekara a duniya sakamakon ta'ammuli da dabobi majinyata.
Ire-iren jinyoyin da mutane kan iya kamuwa dasu daga dabbobi
√ Cutar dake kama da tarin fuka da ake samun ta daga shanu da ake kira da 'Bovine Tuberculosis'
√ Jinyar da ake samu daga jikin mage/kyanwa da ake kira da 'Toxoplasmosis'
√ Jinyar da ake kamuwa da ita ta hangar cizon kare da ake kira da 'Rabies'
√ Jinyar da ake kamuwa da ita ta hanyar 'bera da ake kira da 'Lassa fever'
√ Cututtukan da ake dauka ta hanyar gurbataccen abinci ko abin sha da aka samu 'bullar 'kana nan halittu a ciki da ake kira 'Salmonellosis'
√ Cutar tsutsa da 'karamin hanji ke kamuwa da ita ta hanyar amfani da gurbataccen ruwa da ake kira da 'Ascariasis'
√ Cutar Ebola da ake samu daga jemagu
√ Zazzabin 'zika virus' da ake samu daga cizon wani nau'in sauro da ake kira 'Aedes mosquito'
√ Cutar bacci 'sleeping sickness' da ake kamuwa da ita ta hanyar wani nau'in 'kuda da ake kira 'Tse-tse fly'
√ Jinyar da ake samu ta hanyar cizon kaska da ake kira da 'Lyme disease'
Wadannan kadan ne daga cikin Jinyoyin da ake kamuwa dasu daga dabbobi, a jerin rubuce-rubucen da zamu cigaba da kawo muku akan wannan matsalar zamuyi bayani cikakke akansu daya bayan daya.
Hanyoyin kamuwa da wadannan jinyoyin
Hanyoyin kamuwa da wadannan jinyoyin sun hada da:
√ Mu'amala ta kaitsaye da dabbar da take dauke da 'kwayar cutar bacteria, fungi, parasite da kuma virus da suka hada da:
• Ta'ba abin da ya shafi fitsari, kashi, jini ko yawu na wannan dabbar
• Cizo ko yakushi na dabbar dake dauke da wadancan kwayoyin cutar
√ Mu'amalar da ba takai tsaye ba da majinyatan dabbobi da ya hada da:
• Amfani da kwanon cin abincin dabobin
•Shiga dakin dabobin dake da suke dauke da 'kwayoyin cuta ko kuma barin dabbobin suna yawo a cikin mutane ko kuma suna taba kayan amfanin mutane
√ Ta hanyar 'Kwarin dake daukar cuta su yada irinsu sauro, 'kuda, kaska da sauransu
√ Ta hanyar amfani da nama ko nonon dabbobin dake dauke da jinya a matsayin abinci, ko kuma ta hanyar cin abincin da ya rube ko wanda bai dahu sosai ba da zai haifar da 'bullar wasu 'kananan halittu da zasu cutar da lafiyar dan-Adam.
Hanyoyin kariya daga wadannan jinyoyin
• Rage ta'ammmuli da dabbobin da aka tabbatar da cewa suna dauke da 'kwayoyin cutar da zasu cutar da mutum
• Nisantar cin naman dabbobin da aka tabbatar da cewa suna dauke da jinya
• Kebance dabbobin dake da jinya daga cikin mutane
• Wanke hannu da sabulu yayin da akai ta'ammuli da dabbobi ko kuma yayin da aka shiga wajensu koda ba'a tabasuba
• Kariya daga cizon sauro, kuda ko kaska ta hangar amfani da maganin feshi
• Tabbatar da tsaftar abinci ko abin sha tare da kuma da tsaftar kwanuka, tukwane kafin ayi amfani dasu da kuma bayan angama angama amfani dasu
• Toshe duk wata kafa da 'kananan dabbobi irinsu 'bera zasu shigo cikin gida
• Neman riga kafi kafin kamuwa da jinyoyin da kuma garzawa zuwa asibiti bayan duk wani canji na lafiya da aka ji.
Allah ya 'Kara km karemu
©GHN







